Ministan harkokin wajen kasar Nijar Mohamed Bazoum ya lashen zaben zama shugaban jam'iyyar PNDS-Tarayya bisa rinjayen kuri'u 113 bisa 113, maimakon shugaban kasa Mahamadou Issoufou, bayan wani babban taron jam'iyyar karo na shida da ya gudana a birnin Yamai. Mista Bazoum ya kasance 'dan takarar neman shugabancin jam'iyyar guda, ya rike mukamin mataimakin shugaba kuma shugaban wucin gadi na jam'iyyar tun lokacin da aka zabi Mahamadou Issoufou a matsayin shugaban kasar Nijar a shekarar 2011.
Tun cikin watan Afrilun shekarar 2011, ya rike da kujerar ministan harkokin wajen kasar Nijar.
Zaben na Mohamed Bazoum ya zo daidai lokacin da kawancen jam'iyyun adawa a karkashin inuwar ARDR suka gudanar da wani babban taron gangami kwanan nan a dandalin maharabar majalisar dokokin kasar dake birnin Yamai, inda a cikin jawabinsu suka zargi gwamnatin Mahamadou Issoufou da take sabawa kundin tsarin mulki, haddasa kabilanci da bambanci tsakanin yankunan kasar, tare da janyo tabarbarewar tattalin arzikin kasa. (Maman Ada)