in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta tura jami'an sa ido zuwa Burundi
2015-07-20 10:45:36 cri

Kungiyar hadin kan Afirka ta AU, ta jaddada aniyarta ta tura jami'an sa ido game da kare hakkin bil adama, da kwararru a fannin aikin soji zuwa kasar Burundi.

Hakan a cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ya biyo bayan shawarar da kwamitin tsaronta ya yanke ne, don gane da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka amince da su yayin zaman majalissar kungiyar, mai aikin wanzar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro ko PSC a takaice.

Sanarwar ta kara da cewa, yayin taron majalissar ta PSC na ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne aka amince da tura wakilan kungiyar zuwa Burundi, kudurin da kuma ke kunshe cikin takardar bayan taro ta watan Mayu, da kuma taron da kwararru a fannin tsaro suka gudanar. Ana dai sa ran jami'an masu aikin wanzar da zaman lafiya za su sanya ido game da yanayin da ake ciki a Burundi, yayin da kuma kwararru ta fuskar tsaro za su lura da aikin kwance damarar mayakan sa kai dake kasar, da hadin gwiwar wakilan gwamnati da ma sauran masu ruwa da tsaki.

Tuni dai mahukuntan kasar ta Burundi suka bukaci a dage tura tawagar wakilan ta AU zuwa wani lokaci bayan kammala babban zaben kasar, wanda a baya aka tsara gudanarwa a ranar 15 ga watan nan na Yuli, kafin daga bisani a dage zaben zuwa gobe Talata 21 ga wata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China