in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta shawarta a bude tattaunawar zaman lafiya a Burundi
2015-12-14 13:25:11 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta jaddada damuwarta sosai kan halin da aka ciki a Burundi tare da yin kira ga 'yan kasar da su bude shawarwarin zaman lafiya domin neman wata mafita ga rikicin da ake fuskanta a halin yanzu.

A cewar wata sanarwar kungiyar AU da aka fitar a ranar Lahadi, shugabar kwamitin AU, madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta nuna damuwarta sosai game da tashe tashen hankali a kasar Burundi, musamman hare haren da aka kai a sansanonin sojan dake Bujumbura, hedkwatar kasar Burundi, da kuma yankin karkarar birnin a ranar 11 ga watan Disamba. Jami'ar ta jaddada adawar kungiyar AU wajen yin amfani da tashe tashen hankali, tare da yin allawadai da tashe tashen hankalin keta 'yancin dan adam. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China