in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi allah wadai da ake amfani da makamai masu guba a rikicin Syria
2015-08-28 10:44:44 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi allah wadai da yadda bangarorin da ke gwabza fada a kasar Syria ke amfani da makamai masu guba, inda ya yi kira da a aiwatar da kudurin da kwamitin sulhun majalisar ya cimma game da binciken zargin da ake yi na amfani da wadannan makamai.

Mr Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ta hannun kakakinsa ya kuma ce, abin damuwa ne kan yadda ake kara samun rahotanni game da yadda ake amfani da makamai masu guba da masu yada kwayoyin cuta a rikicin na Syria.

Babban sakatare na MDDr ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin kasar da su hada kai da masu gudanar da binciken da aka tura kasar ta yadda za a samu nasarar aiwatar da kudurin hana amfani da makamai masu guban da aka cimma.

Rahotanni na cewa, mazauna yankin na zargin mayakan IS da yin amfani da makamai masu guba a sabon harin da aka kai a kasar.

A ranar 7 ga watan Agusta ne kwamitin sulhun MDD mai mambobi 15 ya amince da kafa wani kwamitin bincike don zakulo wadanda suka kai hari da sinadarin Chlorine a kasar ta Syria.

Kasar Syria dai ta fada cikin tashin hakali ne a shekara 2011, sakamakon boren kin jinin gwamnatin shugaba Assad da aka kwashe sama da shekaru 4 ana yi ba tare da alamar kawo karshensa ba.

Ya zuwa yanzu sama da mutane miliyan 1 ne aka kashe, kana mutane miliyan 7.6 suka rasa gidajensu, baya ga mutane sama da miliyan 4 da suka bar kasar, sakamakon tashin hankalin da kasar take fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China