in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Somaliya ta ce an harbi 'yan majalisarta 2 bisa kuskure
2015-05-25 10:10:50 cri

Gwamnatin kasar Somaliya ta sanar da cewa, a bisa kuskure ne sojoji suka harbe 'yan majalissar dokokinta guda biyu, inda daya ya hallaka, daya kuma ya samu rauni a ranar Asabar din nan a Mogadishu, babban birnin kasar.

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Mohammed Yusuf ya ce, an harbi 'yan majalissar biyu ne lokacin da suke tuka motarsu daga majalissar bisan kuskuren tantance su. Yana mai bayanin cewa, sojoji suna zargin cewa, wadanda ke cikin motar zai yiwu suna da wata nufi na daban, don haka suka bude masu wuta. Yanzu haka kuma an nada kwamitin da zai binciki wanna lamari ya ba da cikakken bayani.

Wannan al'amarin dai zai zama karo na farko da gwamnati za ta dauki alhakin kisan mamba na majalissar dokoki. Sai dai kuma kungiyar Al-Shabaab tun da farko ta yi ikirarin cewa, ita ce ta harbi 'yan majalissar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China