Ofishin hukumar tsaro na Afrika ta kudu ya tabbatar da cewar, an wawure kudi daga lalitar ofishin hukumar dake Pretoria wanda ya haura dalar Amurka miliyan 3.
Mai magana da yawun hukumar Brian Dube, ya ce, an yi sama da fadi da kudaden ne a ranar 26 ga watan Disambar bara lokacin hutu.
Ya ce, tuni aka kafa kwamitin bincike domin bankado wadanda ke da hannu a badakalar domin su fuskanci shari'a.
A cewar kafofin yada labarun kasar, jam'iyyar COPE ta kasar, ta bukaci ministan tsaro ta farin kaya na kasar David Mahlobo, ya fito fili ya bayyana yadda kudaden suka yi batan dabo.
Jam'iyyar ta nuna shakku kan batun bacewar kudaden da ake danganta shi da 'yan fashi da makami, wanda a cewar su, babu yadda za'a yi barayi su kai ga isa wannan wuri mai matukar tsaro.
An jiyo mai magana da yawun jam'iyyar ta COPE Dennis Bloem, yana cewa, idan har za'a sace kudi a muhimmin wuri kamar helkwatar tsaro ta farin kaya a kasar, to ina makomar rayuka da dukiyoyon jama'ar kasar ta Afrika ta kudu.(Ahmad Fagam)