Mutane goma sha daya ne suka mutu sakamakon tsananin zafi a kasar Afrika ta Kudu, in ji hukumomin kiwon lafiyar kasar a ranar Lahadi.
Dukkan mace macen sun faru a gundumar dake arewa maso gabashi, a cewar ma'aikatar kiwon lafiyar wannan yanki. Wadanda zafin ya halaka masu shekarun aifuwa 22 zuwa 58 ne, in ji kakakin cibiyar Tebogo Lekgothoane. Yawancin mutanen dake fama da tsananin zafi, an karbe su a asibiti. Asibitin guda na yankin gundumar Mahikeng ya karbi mutane 16 a tsawon kwanaki da suka gabata, in ji wannan jami'i. (Maman Ada)