Jam'iyya ANC mai mulki a kasar Afirka ta kudu ta ce, tana goyon bayan shawarar da shugaba Jacob Zuma na kasar ya yanke game da nada Pravin Gordhan a matsayin sabon ministan kudi na kasar.
Kakakin jam'iyyar ta ANC Zizi Kodwa ya ce, jama'a na nuna damuwa game da shawarar da shugaba Zuma ya yanke ta nada mutumin da ba shi da kwarewar da zai iya jagorantar harkokin kudi da kuma manufofin kasar.
Rahotanni na nuna cewa, akwai mummunar baraka tsakanin shugaba Zuma da kuma jam'iyyar ta ANC a cikin 'yan kwanakin nan, inda har ta tilastawa shugaba maido da Gordhan a matsayin ministan kudin kasar, mukamin da ya rike a zamanin gwamnatocin da suka gabata tsakanin shekarun 2009 da kuma 2014.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai shugaba Zuma ya maye gurbin David van Rooyen da ya nada a kan wannan mukami na tsawon kwanaki hudu kacal, bayan da ya kori Nhlanhla Nene daga wannan mukami.(Ibrahim)