Kasar Sin da kasashen Afrika sun zama ainihin abokai, suna da tarihi kusan irin daya, da aikin samun bunkasuwa, da moriyar samun bunkasuwa kusan irin daya, kamar yadda ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya ce , yayin da ya gana da takwaransa na kasar Malawi George Chaponda a ranar 31 ga watan Janairu, yace duk da cewa Malawai ba ta dade da kafa dangantakar diplomasiyya da kasar Sin ba, ministan harkokin wajen Sin ya yada zango na farko ga kasar Malawi, abinda ya nuna cewa, a cikin kasashen Afrika, ko sabuwar kawa ko ta tsohuwa ce, dukkansu manyan abokan kasar Sin ne.
Yanzu, kasashen Afrika na bukatar samun bunkasuwa cikin dogon lokaci da kansu, da gaggauta raya masana'antu da aikin gona na zamani, sabo da haka, suna da bukatar yin hadin gwiwa da kasar Sin a wadannnan fannoni. Kamar yadda shugaban kasar Malawi ya nuna fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen kafa tashoshin samar da wutar lantarki, da gina filin jiragen sama da shimfida layin dogo. Yayin da firaministan kasar Mauritius yana sa ran inganta hadin gwiwa da kasar Sin game da tattalin arziki a fannin cin gajiyar albarkatun teku, kuma yana maraba da masu yawon shakatawa na Sin da su kai ziyara a kasar. Haka kuma, kasar Mozambique tana fatan yin hadin gwiwa da Sin game da makamashi, da muhimman ababen more rayuwa, da kirkire-kirkire, da aikin gona, yayin da kasar Namibiya tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin game da wutar lantarki da makamashi.
Kasashen Afrika na gaggauta samun bunkasuwa, sabo da haka, akwai makoma mai haske wajen yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.(Bako)