A cikin dogon lokaci, kasar Sin da kasashen Afrika sun tsaya tsayin daka kan samun moriyar hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, da yin amfani da fiffikon amincewar juna a fannin siyasa da taimakawar juna a fannin tattalin arziki. Tun daga shekarar 2009, kasar Sin ta zama babbar kasa ta farko wajen yin cinikayya da kasashen Afrika. Kasashen Afrika su ma sun zama wuraren da Sin ta yi gine-gine a kasashen waje, kuma akwai masana'antun Sin sama da 3000 da suka saka jari a kasashen Afrika, kuma sun samar da guraben aikin yi sama da dubu 100. Ya zuwa watan Satumban shekarar 2015, Sin ta ba da tallafi da tattara kudade don shimfida hanyoyin jiragen kasa da tsawonsa ya kai kilomita 5675, da hanyoyi da tsawonsa ya kai kilomita 4507 a kasashen Afrika. Ban da wannan kuma, jimillar kudin cinikayya dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta karu sosai,har ta kai dalar Amurka biliyan 210 a shekarar 2013, yayin da wannan adadi bai wuce miliyan 12 a shekarar 1950 ba. A shekarar 2014, firaministan Sin Li Keqiang ya ziyarci Afrika, inda ya gabatar da manyan ayyuka a fannoni 6 da raya hadin gwiwa game da layin dogo da hanyoyin mota da na jiragen sama, abun da ya tsara shiri game da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.
Kwararre a fannin tattalin arziki na jami'ar Nairobi da ke kasar Kenya Ikiyala ya ce, kasar Sin, ta taka muhimmiyar rawa game da hadin gwiwar tattalin arziki da siyasa. A matsayin gamayyar tattalin arziki ta biyu a duniya, kasar Sin ta samu muhimmin matsayi wajen inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da Afrika.