Ban da wannan kuma, kasar Sin da kasashen Afrika suna taimakawa juna game da harkokin tsaro, Sin ta tashi tsaye don shiga cikin aikin samar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afrika, kuma ta nuna goyon baya game da gaggauta raya nahiyar da kawar da talauci da cimma burin samar da dauwamammen zaman lafiya. A watan Satumbar bara, yayin da shugaban Xi ya halarci tarurrukan koli don murnar cika shekaru 70 da kafa M.D.D., ya gabatar da wasu shawarwari game da kyautata aikin samar da zaman lafiya na M.D.D. Bisa kudurorin M.D.D., Sin ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya a kasashen Kongo(Kinshasa), Mali, Liberiya, da Sudan ta Kudu da dai sauran kasashe, wadanda suka ba da babbar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya a zamantakewar al'umma, da samun wadata a fannin tattalin arziki, kuma sun samu babbar jinjinawa daga jami'an M.D.D. Jami'in M.D.D. dake kasar Liberiya Salihu Uba ya ce, sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin sun sauke nauyin da ke wuyansu, kuma sun taka rawar a zo a gani, don ba da nasu gudummawa game da samar da zaman lafiya da wadata a kasar Liberiya.
Dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa ta shafi jama'a, sabo da haka, kasar Sin da kasashen Afrika sun yi musayar al'adu, kana sun yi koyi da juna a wannan fanni, Sin ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin al'adu da dukkan kasashen Afrika da suka kafa dangantakar diplomasiyya da Sin. A ko wace shekara, gwamnatin Sin tana ba da kyautar kudin karatu ga mutane sama da 7000 a kasashen Afrika, kuma a ko wace shekara, Sin tana shirya tarurrukan kara-wa-juna-sani sama da 100 na bangarorin biyu ko bangarorin daban daban don horar da manyan jami'ai zuwa kasashen Afrika, yanzu Sin ta bada tallafi ko ba da rancen kudi don an kafa makarantu sama da 200 a kasashen Afrika.