in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna sahihiyar zuciya wajen sada zumunta da kasashen Afrika
2016-02-24 09:21:47 cri


Daga ranar 30 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Febrairu wannan shekara, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Malawi, Mauritius, Mozambique, da Namibiya, kuma wannan shi ne ziyara ta farko da ministan ya yi a bana, kuma wannan itace shekara ta 26 da ministan harkokin wajen Sin ya ziyarci kasashen Afrika a farkon wata shekara, abinda ya nuna a fili matsayi na musamman da kasashen Afrika ke da shi a cikin sha'anin diplomasiyyar kasar Sin, musamman game da yadda kasar Sin ke raya alakarta da kasashen Afrika.

Dalilin ziyarar ta Mista Wang a kasashen Afrika a wannan karo shi ne, don gudanar da sakamakon da aka samu a yayin taron kolin na tattaunar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika da aka yi a birnin johannesburg a watan Disambar bara, musamman ma bayan da shugaba Xi ya gabatar da tunanin raya dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika don ta zama dangantakar abokantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da sabbin tunanin raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, da shirin raya hadin gwiwa a fannoni 10 cikin shekaru 3 masu zuwa, kuma za a bi wannan alkibla don raya hadin gwiwar moriyar juna da samun bunkasuwa tare.

Tun daga shekarar 1991, ministan harkokin wajen Sin na wancan lokaci Qian Qichen, ya ziyarci kasashen Habasha, Uganda, Kenya da Tanzaniya a farkon shekarar, daga bisani ministocin harkokin wajen Sin da suka biyo bayansa, sun yi ta ziyarar kasashen Afrika a farkon wata shekara. Ministan harkokin wajen Sin da takwarorinsa na kasashen Afrika sun tattauna don sada zumunci, da yin hadin gwiwa don samun bunkasuwa tare, gwamnatocin kasashen Afrika da jama'arsu na wadannan kasashen Afrika da ministocin kasashen Afrika suka ziyarta, sun dora muhimmanci sosai game da ziyarar, kuma an samu sakamako mai gamsarwa.

A cikin shekaru 26 da suka gabata, ko da yake, yanayin da kasashen duniya ke ciki na samun bunkasuwa a kullumyaumin, amma raya alakarta da kasashen Afrika ya zama tushen aikin diplomasiyyar kasar Sin, kuma Sin ta nuna goyon baya sosai ga al'ummar Afrika da su warware batutuwan da kansu. A cikin shekaru 26 da suka gabata, kasar Sin da kasashen Afrika sun samu babban ci gaba, kuma hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin biyu ya samu inganci. A fannin siyasa, kasar Sin da kasashen Afrika sun kafa amincewar juna cikin daidaito, kuma hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu ya samu karfafa. Kasar Sin da kasashen Afrika suna mayar da kowanensu a matsayin wani babban jigo wajen raya dangantakar kasashen biyu, kuma game da babbar moriyar kasar Sin da kasashen Afrika sun nuna wa juna goyon baya. A shekarar 2013, bayan da shugaban Xi ya hau karagar mulki, ya zabi kasashen Afrika don fara ziyara, inda ya gabatar da manufar nuna sahihiyar zuciya, da gudanar da hakikanin hadin gwiwa da sada zumunta ga kasashen Afrika, abun da ya nuna hanyar raya alakar Sin da kasashen Afrika. Kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Malawi George Chaponda ya ce, Sin ta zama ainihin abokiyar kasar, wadda ta taimakawa kasar don cimma burin samun bunkasuwa cikin dogon lokaci da kanta, kuma ta nuna mata goyon baya game da raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma da sauransu. Shawarwarin da Sin ta gabatar a yayin taron kolin na tattaunawar hadin gwiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a birnin johannesburg ya sa kasashen Afrika sun fahimci makoma mai haske wajen samun bunkasuwa.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China