Tawagar ayyukan wanzar da zaman lafiya ta MDD da AU UNAMID a ranar Litinin din nan 8 ga wata, ta yi gargadin tabarbarewar rikici a Kalma, babban sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Darfur na kasar Sudan.
Kamar yadda ta bayyana a cikin wata sanarwa, zaman fargaba ya fara ne tun daga makon jiya wato 4 ga wata bayan da wasu 'yan sandan Sudan suka shiga sansani, inda suka ratsa tsakiyar sansanin da mota, abin da ya sa wasu daga cikin masu gudun hijira suka nuna rashin amincewarsu, tare da gudanar da zanga-zangar adawa har ya kai ga aka yi harbin bindiga.
Tawagar ta jaddada muhimmancin kiyaye doka daga dukkan bangarori a ciki da wajen Kalman, tana mai nuni da cewar, nauyi ne da ya rataya a kan wuyan ko wane bangaren na tabbatar da samar da yanayi mai kyau na zamantakewa a sansanonin.
Har ila yau, tawagar ta UNAMID ta bukaci mahukunta da su mutunta 'yancin dan Adam da dokoki, a kuma guji duk wani nau'in amfani da karfi ko rashin mutunci. (Fatimah)