in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta kafa dokar kudi na addinin musulunci nan da karshen wannan shekara
2016-02-18 11:14:32 cri

Gwamnatin kasar Kenya a ranar Larabar nan ta ce, za ta fara amfanin da dokar kudi na addinin musulunci zuwa nan da karshen shekarar nan ta 2016.

Babban mai shari'ar kasar Farfesa Githu Muigai wanda ya sanar da hakan a wani taron musulunci da aka yi a birnin Nairobi ya ce yanzu haka ana tuntubar masu ruwa da tsaki domin a fitar da tsari na karshe.

Babban mai shari'ar a cikin jawabin shi a lokacin taron dokokin kudi na musulunci a gabashin kasashen Afrika na shekara ta 2016 da aka yi a birnin na Kenya ya ce, suna fatan gabatar da dokar a gaban majalissar dokokin kasar nan da 'yan watanni masu zuwa, ta yadda dokar za ta fara aiki nan da karshen shekarar da ake ciki.

Taron na yini daya ya samu mahalartar sama da 200 da suka tattauna damammmakin dake tattare da dokar kudin na musulunci.

Farfesa Muigai ya ce, duk da cewar tsarin shari'ar kasar an kara inganta shi a cikin shekaru, har yanzu yana bukatar muhimman canji da suka hada da shari'ar kudi na addinin musulunci ya cimma matsayin shi. A shekara ta 2008 Kenya ta yi kwaskwarima kan dokokin bankunanta don ba da dama ga bankunan musulunci gabatar da ayyukan su.

Babban mai shari'ar ya ce, sabbin dokokin za su inganta bangaren harkokin kudi na musulunci da yanzu haka ake da su. Za'a yi nazari cikakke na dokokin da a yanzu haka ake da su don a samu cike gurbin wadanda ke da bukatar hakan.

Ya kara da cewa, sabuwar dokar za ta ba da 'yancin ga baitulmalin kasar su fadada bankunan shari'ar musulunci wanda shi ma wata hanya ce ta samun kudi.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China