in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon Sin ya yi kira da a farfado da shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palesdinu
2016-01-27 09:44:48 cri

Manzon kasar Sin a MDD a ranar Talatan nan ya yi kira ga hukumomin kasa da kasa da su kara daukan matakai da kuma farfado da shirin samar da zaman lafiya, ta yadda za'a kawo Isra'ila da Palesdinu a kan teburin shawarwari.

Liu Jieyi, wakilin din din din na kasar Sin a MDD ya yi wannan kiran ne a taron da kwamitin tsaron majalisar ya yi game da yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya ce, tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palesdinu ya tsaya cak, ga karuwan tashin hankalin da ake fuskanta da tsanantan yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya ce, kasashen duniya ya kamata su bukaci bangarorin biyu duka da su dauki matakan da suka dace cikin gaggawa domin sassauta halin da ake ciki.

A matsayin kasar dake da rinjaye, ya kamata Isra'ila ta yi jagora a wannan kokari, kuma a kara mai da hankali kan tsaro a yankin.

Wakilin na kasar Sin ya kuma yi kira ga kwamitin tsaron da ya yi tunanin samar da kariya daga kasa da kasa ga Palesdinawa.

Ya ce, domin a samu inganta yanayin rayuwan al'ummar Palesdinu, kasar Sin ta yi shawarar samar da taimakon kudin da ya kai kimanin yuan miliyan 50. Sannan kuma a shirye take tare da sauran kasashen duniya ta aikatar da aikin ingiza samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China