Kakakin babban magatakardan MDD Stephane Dujarric, ya bayyana a jiya Litinin cewa, Ban Ki-Moon ya kalubalanci kasashen Saudiyya da Iran da su kauce wa daukar matakai da ka iya kawo barazana ga dangantakar dake tsakanin su.
Mista Dujarric, ya bayyana hakan ne a wajen taron manema labaru cewar, Ban Ki-Moon ya yi shawarwari da ministan harkokin waje na kasar Iran Mohammad Javad Zarif da kuma takwaransa ministan harkokin waje na kasar Saudiyya Adel al-Jubeir ta wayar tarho. Inda Mista Ban ya yi Allah wadai da farmakin da aka kai kan ofishin jakadancin kasar Saudiyya dake Tehran, ya kuma yi kira ga kasar Iran da ta dauki matakan kare hukumomin diplomasiyya dake kasar ta, sannan ya nuna damuwa dangane da batun yanke huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
Bugu da kari, Stephane Dujarric ya bayyana cewa, manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batun kasar Sham Staffan de Mistura yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Riyadh, hedkwatar kasar Saudiyya, daga bisani, zai kai ziyara a kasar Iran. A yayin ziyararsa a Riyadh, zai yi bincike kan tasirin da batun kasashen Saudiyya da Iran ya kawo wa yunkurin siyasa na kasar Sham. Ya kuma bayyana cewa, dole ne a dauki matakan magance lalacewar yanayin a yankunan kasashen biyu bayan afkuwar wannan al'amari.(Lami)