in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta bukaci a warware rikicin Syria ta hanyar siyasa
2016-02-14 10:17:49 cri

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bayyana cewar, za'a iya warware rikicin Syria ne ta hanyar makatai irin na siyasa, sannan ya bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar da su yi kyakkyawan amfani da wannan damar domin kawo karshen tashin hankalin da ya sukurkuta kasar.

Kerry, ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya gabatar a yayin wani babban taro da aka shirya da nufin warware rikicin Syriar a Munich. Jami'an diplomasiyya na kasa da kasa sun cimma matsaya, inda suka bukaci bangarorin kasar ta Syria da su yi kyakkyawan amfani da damar tattaunawa domin warware dambarwar siyasar da ta dabaibaye kasar.

Kerry ya kara da cewar, muddin kasashen duniya da al'ummar Syriar ba su yi kyakkyawan amfani da wannan damar ba, to rikicin kasar zai ci gaba da ta'azzara.

Sannan, ya bayyana bukatar a gaggauta shigar da kayayyakin tallafi a kasar ba tare da bata lokaci ba, duk da cewar akwai jan aiki na tabbatar da tsakaita wuta a kasar a cikin mako mai zuwa.

Ya ce, babban al'amari da ya kamata a fayyace shi ne batun matakan da ya kamata a dauka kan 'yan ta'adda da wanda bai dace a dauka ba.

Amurkar ta zargi Rasha da kaddamar da hare hare daga sama kan masu adawa da gwamnatin Syria a maimakon 'yan ta'adda. Sai dai Rashar, ta sha musanta wannan zargi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China