in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kakabawa wasu kamfanonin dake taimakawa gwamnatin Syria takunkumi
2014-07-10 10:37:41 cri

Kasar Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni uku a ranar Laraba dake taimakawa gwamnatin Syria, wanda daya daga cikinsu na da cibiya a daular kasashen Larabawa. Matakin na hukumonin Amurka ya shafi kamfanin Pangates dake daular kasashen Larabawa, da kuma kamfanonin Expert Partners da Megatrade, da Amurka take ganin na Syria ne. Haka kuma matakin ya haramtawa 'yan Amurka yin kasuwanci tare da wadannan kamfanoni da tuni suke cikin jerin haramtattun kamfanoni a idon Amurka, tare da rike kudadensu dake cikin bankunan Amurka. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China