in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya gana da shugaban 'yan adawan Syria domin nuna goyon baya
2014-05-14 15:04:46 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya gana da shugaban babbar kungiyar 'yan adawa ta kasar Syria a wani matsayi na nuna goyon bayan Amurka ga 'yan adawar kasar Syria, wacce yaki ya daidaita.

A jiya Talata da yamma ne Obama, shi ma ya shiga cikin taron, wanda mai bayar da shawara kan harkokin tsaron kasar Amurka Susan Rice take gudanarwa da shugaban hadaddiyar kungiyar 'yan adawa na kasar Syria, shugaba Ahmad Jarba da wata tawaga mai wakiltar 'yan adawar ta Syria, kamar dai yadda wata sanarwar fadar White House dake Washington ta bayyana.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Amurka ta White House, ta ce, Obama ya yi marhabin da shugabancin hadaddiyar kungiyar 'yan adawar da kuma kyakkyawan matakin da take dauka na gudanar da tattaunawa, daga nan kuma, Obama ya baiwa hadaddiyar kungiyar 'yan adawan karfin gwiwa da su kara kokari na ganin kungiyarsu ta cimma gurinta na samar da gwamnati da za ta wakilci daukacin al'ummar Syria. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China