in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka na shawarta baiwa 'yan adawar Sham karin taimako
2014-02-19 10:44:28 cri

Rahotannin baya bayan nan na cewa, shugaba Barack Obama na Amurka, na duba yiwuwar fara biyan albashi ga wasu 'yan adawar kasar Sham, tare da samar musu hanyoyin saukaka sufuri, da samun bayanan sirri.

Hakan dai kamar yadda jaridar New York Times ta rawaito, na da nufin baiwa 'yan adawar da aka tantance karfin gwiwar cimma nasarar da suka sanya a gaba, a dauki ba dadin da suke yi da dakarun gwamnati, da kuma yayin zaman tattaunawar sulhu.

Baya ga wannan, shugaba Obama da wasu shuwagabannin kasashen yamma, sun cimma kudurin jingine batun hana baiwa wani sashe na 'yan adawa tallafin wasu nau'o'in makamai. Matakin da zai ba da damar rungumar shawarar da kasar Saudiyya da wasu kasashe suka bayar a baya, ta samar da irin wadancan makamai ga 'yan adawar da aka tantance. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China