HCR ta kwashe 'yan gudun hijirar Somaliya fiye da 6000 daga wani sansanin 'yan gudun hijira dake Kenya
'Yan gudun hijiran Somaliya fiye da 6000 sun koma kasarsu bisa son ransu daga sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab dake arewacin Kenya, a karkashin taimakon hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (HCR). A cewar wani rahoton da HCR ta fitar a ranar Laraba, mutane 248 sun koma Mogadishu da Baidoa dake kudu maso yammacin ta hanyar jirgin sama a cikin watan Disamba. A ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2015, kusan 'yan gudun hijirar Somaliya 6,101 suka koma kasarsu tun daga ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2014, wato lokacin fara gudanar da shirin HCR wanda ke nufin taimakawa kwashe 'yan gudun hijirar Somaliya masu son komawa kasarsu daga kasar Kenya. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku