in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi alla wadai da harin da aka kai a wani otel dake Somaliya
2016-01-23 13:40:23 cri
A ran 22 ga wata, kwamitin sulhun MDD ya mika wa kafofin watsa labaru wata sanarwa, inda ya yi tir kan harin ta'addanci da aka kai wa wani otel din dake Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya.

Wannan sanarwa ta jaddada cewa, dole ne a yanke hukunci kan masu kai harin. Kuma ya nemi a dauki kwararan matakan toshe hanyoyin samun kudi na kungiyar Al Shabaab da sauran kungiyoyin ta'addanci.

Bugu da kari, wannan sanarwa ta sake bayyana cewa, kowane irin harin ta'addanci da ake kai ba zai girgiza niyyar kwamitin sulhu na MDD na kokarin shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Somaliya ba, kwamitin yana fatan babban zaben da za a yi a kasar Somaliya zai taka rawa wajen dawo da zaman lafiya a kasar. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China