in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin 'yan Najeriya da suka mutu a turmutsitsin Saudiya ya kai 64
2015-09-30 09:45:18 cri

An tabbatar da ya zuwa yanzu 'yan Najeriya wadanda suka mutu sanadiyar turmutsitsin da ya faru lokacin aikin Haji a kasar Saudiya a makon jiya sun kai 64, bayan da aka sake gano gawawwakin wadansu guda 10.

Kamar yadda wani kakakin hukumar ayyukan haji na kasar Uba Mana ya tabbatar,, har yanzu ana kan neman wadansu 'yan kasar 244 da suka bace sakamakon hadarin.

Jami'in ya ce, an samu karin wadansu 'yan kasar 10 da suka ji rauni, abin da ya sa adadin wadanda suka ji rauni ya kai 71 maimakon 61 da aka bayyana tun da farko.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China