Wakilin Sin na musamman kan al'amurran yankin Gabas ta Tsakiya Gong Xiaosheng, ya fada a Lahadin nan cewar, kasar Sin tana goyon bayan al'ummar Palasdinawa da kuma shirin samar da zaman lafiya a yankin.
Wakilin, ya furta hakan ne ga manema labaru a birnin Ramallah dake gabar yammacin kogin Jordan, yayin wata ziyara inda ya bayyaba cewar, bai kamata ba a mayar da al'ummar Palasdinawa tamkar saniyar ware, kuma kasar Sin tana goyon bayan kafa yantacciyar kasar Palastinu mai ikon cin gashin kanta.
A cewar mista Gong, ziyarar kwanan nan da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai a yankin Gabas ta Tsakiya, wasu alamu ne dake nuna sabuwar dangantaka tsakanin kasar Sin da Palastinu, dama sauran kasashen dake shiyyar.
Ziyarar wacce ita ce ta farko ta rangadin shugaban a shekarar 2016, kuma ita ce ziyararsa ta farko a yankin tun bayan darewarsa kujerar shugabancin kasar. A lokacin da shugaba Xi ke gabatar da jawabi a taron kasashen Larabawa a birnin Alkahira, babban sakon dake kunshe cikin jawabin nasa shi ne, batun aniyar kasar Sin na tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali da kuma samun bunkasuwa.(Ahmad Fagam)