in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a baiwa Palastinawa daga Syria matsugunai a yammacin gabar kogin Jordan
2015-09-07 10:35:00 cri

Ma'aikatar harkokin wajen Palastinu ta fada a ranar Lahadin nan cewar, ta kammala shiri tsab domin karbar bakuncin Palastinawa 'yan gudun hijira, musamman wadanda rikicin Syria ya daidaita domin ba su matsugunai a yammacin gabar kogin Jordan.

Ma'aikatar ta ce, duk da ka san cewar, tana fuskantar matsalar karancin kudade, amma ta sha alwashin cewar, za ta bude dukkannin gidajen al'ummar Palastinawa a yammacin gabar kogin Jordan domin tseratar da rawuwarsu.

Ma'aikatar harkokin wajen ta ce, dama dai Palastinawan na da 'yancin zama a kasarsu, kuma bai dace a tilasta su barin muhallansu ba, ko kuma su dinga watangaririya daga wancan sansanin 'yan gudun hijira zuwa wancan ba.

To sai dai kuma 'yan siyasar kasar Isra'ila na da mabambantan ra'ayi kan batun yadda Isra'ilan za ta tunkari batun 'yan gudun hijirar da rikicin Syria ya daidaita.

Yayin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke bayyana cewar, ba za su amince da baiwa 'yan gudun hijirar Syria mafaka ba domin a shekaru 4 da suka gabata, sun agaza wadanda yakin basasa ya tarwatsa, amma a halin yanzu Isra'ila ba ta da wurin tsugunar da 'yan gudun hijirar kasancewar Isra'ilan, ba ta da fadin kasa.

A bangare guda, madugun 'yan adawar kasar Isaac Herzog ya ce, bai ga dalilin da zai sa Netanyahu ya shafawa fuskar shuni ya ki amincewa da 'yan gudun hijarar ba wadanda ke dauke da yara kanana a hannayen su suna neman tsira da rayuwarsu.

Da ma dai a karshen wannan makon ne shugaban Palastinwa Mahmoud Abbas ya bukaci MDD da kungiyar tarayyar Turai wato EU da su matsa lamba ga gwamnatin Isra'ila domin kyale Palastinawa 'yan gudun hijira su koma matsugunnansu dake yammacin gabar kogin Jordan.

Bugu da kari kungiyar fafutukar 'yancin al'ummar Palastinawa wato PLO ta ce, tana aiki tukuru domin ganin ta dakile yunkurin tsallakawar Palastinawa zuwa Turai don neman mafaka.

Kamar yadda mamban kwamitin gudanarwar kungiyar ta PLO Ahmed Majdalani ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Asabar din nan cewar, rayuwar 'yan gudun hijirar dake tsallakawa Turai na cikin fargaba sakamakon hasarar daruruwan rayukan da ake fuskanta a yunkurinsu na tsallakawa kasashen Turai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China