in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Falasdinawa ya yi watsi da batun raba masallacin al-Aqsa
2015-09-17 10:09:55 cri

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya ce, ba za su amince da duk wani yunkuri na raba masallacin al-Aqsa gida biyu ba. Abbas ya bayyana hakan ne yayin wani zaman shawarwari a birnin Ramallah, taron da kusoshin Falasdinawa dake zaune a gabashin birnin Kudus suka halarta.

Mahmoud Abbas ya ce, wajibi ne birnin Kudus ya zamo helkwatar kasar Falasdinu. Kaza lika a cewar sa masallacin al-Aqsa na musulmi ne da kiristoci, don haka ba za su baiwa Yahudawa dama ta keta alfarmar sa ba.

Shugaba Abbas ya kara da cewa, Falasdinawa za su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, na dakile aniyar Yahudawan Isra'ila game da birnin Kudus.

Yanzu haka dai kura ta lafa, bayan tarzomar kwanaki 3 tsakanin Falasdinawa da 'yan sandan Isra'ila a yankin gabashin birnin na Kudus. Falasdinawa dai na zargin Yahudawan Isra'ila da yunkurin raba masallacin al-Aqsa tsakanin musulmi da Yahudawa masu bauta.

Tun cikin shekarar 1967 Isra'ila ta mamaye sassan birnin Kudus, bayan da ta yi ikiranin cewa, tun fil azal, yankin mallakar Yahudawa ne. A kuma shekarar 1968, Isra'ilan ta amince da sakin yankin gabashin birnin, sai dai duk da hakan, kasashen duniya da dama ba su amince da halascin birnin na Kudus a matsayin helkwatar kasar Isra'ila ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China