in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kare taron AU tare da alkawarin cimma burin muradin 2063
2015-06-16 10:06:12 cri

An kammala taron kungiyar AU karo na 25 da sanyin safiyar Talatan nan a birnin Johannesburg, tare da alkawarin cika burin muradin 2063, wani jadawalin ci gaba na nahiyar baki daya.

A lokacin taron yini biyun, shugabannin kasashe da gwamnatocin Afrika sun tattauna muradin na 2063, samar wa mata aikin yi, rigingimun siyasa a Burundi, tayin shirin ciniki cikin 'yanci a nahiyar, da kuma hanyoyin samun sabbin kafofin kudaden tafiyar da ayyukan kungiyar.

Tun farko kafin fara shi sai da aka fara zaman tattaunawa a matakan ministoci da jami'ai tun daga ranar 7 ga watan Yunin.

Sai dai a lokacin taron, hankali ya koma a kan shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir wanda yake cikin mahalarta, kuma kotun sauraron kara ta duniya ICC take neman shi bisa zargin laifukan take hakkin bil adama. Yanzu haka an saka kasar Afrika ta Kudu a gaba bisa laifin kin kama al-Bashir, ganin yadda ya yi barin da sammacin da aka kai mashi.

Amma shugaban kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta kare wannan shawarar da aka yi ta gayyatar shugaba al-Bashir zuwa wajen taron a gaban manema labarai, inda ta ce, Sudan mamba ce ta kungiyar AU, kuma a ko da yaushe tana halartar duk wani sha'ani da aka gayyace ta, kuma kungiyar AU, in ji ta, tana ayyukanta ne bisa tsarinta, ba bisa tsarin kotun duniya ta ICC ba.

Taron dai, an yi shi ne karkashin taken ''shekarar samar wa mata aiki da ci gaba zuwa ga muradin Afrika na 2063''. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China