Shuwagabannin kasashen mambobin kungiyar hadin kan Afirka AU, sun tattauna game da hanyoyin samar da kudade, wadanda za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirye-shiryen kungiyar.
Mataimakin shugabar hukumar zartaswar kungiyar ta AU Erastus Mwencha ne ya bayyana wa manema labarai hakan a jiya Lahadi, bayan kammala taron kungiyar karo na 26, wanda ya gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha.
Mr. Mwencha, ya ce, yayin zaman da aka kammala a ranar Asabar, mambobin kungiyar sun nazarci rahoto game da karin hanyoyin samar da kudaden gudanar da ayyukan ci gaban kungiyar, ayyukan dake kunshe cikin kasafin kudin bana wanda aka amince da shi. Kaza lika sun daddale tsarin da za a bi wajen raba kasafin kudin tsakanin su.(Saminu)