Firaministan kasar Togo Selom Klassou, wanda aka nada a ranar 10 ga watan Juni, ya gabatar a ranar Lahadi da mambobin gwamnatinsa da ke kunshe da ministoci 22, inda a cikinsu akwai mata hudu.
Sabuwar gwamnatin dai na kunshe da tsoffin ministoci goma sha biyu na gwamnatin da ta shude, da sabbin ministoci goma. A cikin tsoffin ministocin, akwai Guy Lorenzo na ma'aikatar sadarwa, Payadowa Boukpessi na hukumar kula da fadin kasa, da kuma Kossi Assimaidou, ministan harkokin gida, tattalin arziki da kudi, da ke kula da fasali da makomar kasa. Haka kuma wannan sabuwar gwamnatin na kunshe da mata hudu, inda madam Tchabilengui Kolani Yantchare, sabuwar shigowa dake rike da kujerar kula da harkokin jama'a, kare mata da yaki da jahilci. (Maman Ada)