Sararin samaniyar kasashen Togo da Benin, da ke karkashin kulawar kasar Ghana tun yau da kusan shekaru saba'in, yanzu ya koma a karkashin hannun cibiyar tsaro da zirga zirgar jiragen sama a Afrika da Madagascar (ASECNA), a cewar gidan talabijin din kasar Togo (TVT) a ranar Alhamis.
A cewar kakakin reshen ASECNA, Amaou-Talle Emmanuel, kasashen Togo da Benin yanzu su ne da ke da iko kan sararin samaniyarsu, lamarin da ke baiwa ASECNA damar kulawa da wannan sararin samaniya da kasashen mambobin suka mika hannunta. (Maman Ada)