Shugaban bankin ci gaban Afrika ADB Akinwumi Adesina, ya nuna yabo a ranar Litinin kan bunkasuwar tattalin arziki a kasar Togo, tare da yin alkawarin ba da jerin tallafi ga bangaren ma'adinai, musammun ma ga mata da samar da ayyukan yi a wannan kasa.
Mista Adesina ya isa birnin Lome, inda ya samu tattaunawa tare da shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe, musammun ma kan shirin ci gaba na shekarar 2016 zuwa 2020 na kasar.
Kasar Togo ta samu ci gaban tattalin arziki a tsawon shekaru biyar na baya bayan nan, inda ya karu bisa kiyasin bunkasuwar GDP da kashi 5,8 cikin 100 a shekarar 2014.
Da yake bayani a gaban manema labarai, shugaban ADB ya bayyana jin dadinsa kan bunkasuwar tattalin arziki a kasar Togo.
Mista Adesina ya tunatar da cewa, Togo na amfana sosai da banki, inda ba da dadewa ba, ta samu dalar Amurka miliyan 17 domin tallafawa wani shirin gwamnatin kasar dake shafar samar da ayyukan yi ga matasa dubu 20.
Har ila yau, shugaban ADB, ya yi alkawarin wani tallafi domin ingiza bangaren hakar ma'adinai, da kuma wani tallafi mai yawa daga asusun kasa na FNFI da gwamnatin Togo take gudanar da aikinsa. (Maman Ada)