Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, ta bukaci a bullo da shirin tada komadar matsalolin zamantakewa da siyasa da tattalin arziki wadanda cutar Ebola ta haddasa.
AU ta gabatar da bukatar daukar matakan farfado matsalolin da aka fuskanta ne a yayin taronta na kwanan nan, inda ta bukaci a bullo da wani shirin da zai cike gibin da aka samu sakamakon barkewar cutar ta Ebola a kasashen yammacin Afrika 3 wato Guinea, da Liberiya da kuma Saliyo.
Kungiyar ta gamsu da kokarin da ake yi wajen yakar cutar, sannan ta yaba wa kasahen da matsalar ta fi kamari dangane da irin jazurcewar da suka yi domin fatattakar cutar daga kasashen, har ma kokarin da suke yi bayan kawar da cutar.
AU ta bukaci kasashen 3 da matsalar ta fi ta'azzara da kada su yi kasa a gwiwa wajen yaki da cutar, kuma ta bukace su da su ci gaba da daukar matakan da suka dace har zuwa lokaci da kasashen za su kasance babu alamar burbushin cutar Ebola baki daya.
A yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, jami'in kungiyar AU Mustapha Sidiki Kaloko, ya ce, kungiyar za ta mai da hankali wajen gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar al'ummomin kasashen da cutar Ebolan ta fi shafa.
Kungiyar ta bukaci a tallafa wa kasashen wajen sake inganta asibitocinsu domin magance samun bullar cutar a nan gaba, da kuma tada komadar da kasashen 3 suka fuskanta a sakamakon barkewar cutar.(Ahmad Fagam)