Wasu shaidun gani da ido sun ce, wasu da ake zargin barayin shanu ne suka kashe a kalla mutane 35 a yankin Shiroro ta jihar Nijar dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya kamar yadda dagacin kauyen ya shedawa kamfanin dillacin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Alhamis din nan.
Daga cikin wadanda iftila'in ya rutsa da su, akwai dagacin kauyen Allawa dake yankin na shiroro da sifeton 'yan sanda da kuma wasu mutane 33, kamar dai yadda wani dagaci a yankin wanda ya neme a sakaye sunansa ya shedawa kamfanin dillancin labaran na Xinhua ta wayar hannu.
Shugabanin al'ummar yankin sun ce, adadin maharan ya kai 40, kuma sun yi amfani ne da muggan makamai da bindigogin masu sarrafa kansu da kansu, sannana sun cinnawa gidaje sama da 25 wuta, kuma an yi amanna maharani Fulani ne.
Dagacin kauyen ya ce, yanzu haka mazauna kauyen duk sun fantsama a sakamakon kazamin harin.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jahar Nijar Bala Elkana, ya ce, rundunar ta tabbatar da afkuwar lamarin, kuma lamarin ya faru ne a daren Talatar din nan, sai dai ya ce, har yanzu ba su kammala tantance adadin mutanen da harin ya rutsa da su.(Ahmad Fagam)