in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Turkiya ba za su fice daga Iraki ba, in ji shugaban kasar
2015-12-28 10:32:10 cri

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya, ya saba alkawarin da ministan harkokin wajen kasarsa ya furta, inda ya sake nanata cewa, dakarun kasarsa ba za su fice daga yankunan kasar Iraki ba.

Shugaba Erdogan wanda ya bayyana hakan jiya a birnin Istanbul ya ce, dakarun Turkiyar suna samar da tsaro da kuma horo ne ga dakarun Kurdawa da na Larabawa, don haka za su ci gaba da zama a yankunan arewacin kasar ta Iraki.

A farkon wannan watan nan ne kasar Turkiya ta tura daruruwan sojoji zuwa sansanin Bashiqa da ke arewacin kasar ta Iraki, abin da Turkiyar ta ce wani mataki ne na matakan da kasashen duniya ke dauka na samar da horo da makamai ga dakarun Iraki a yakin da suke yi da kungiyar IS.

Ko da yake kasar Iraki ta yi Allah-wadai da wannan mataki na Turkiya, har ma ta gabatar da batun gaban kwamitin sulhu na MDD don ganin ta janye dakarun nata daga yankunan kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China