A jimilce, 'yan kasar Iraki 714 aka kasha, kana 1269 suka jikkata a cikin hare-haren ta'addanci, tashe-tashen hankali da yake-yake a cikin watan Oktoba, in ji kakakin MDD, Stephane Dujarric a ranar Litinin a cibiyar majalisar dake birnin New York.
A yayin taron manema labarai nan, mista Dujarric ya ambato kalaman Jan Kubis, manzon musamman na sakatare janar na MDD game da Iraki, dake bayyana cewa, wadannan alkaluma na nuna walhalhalun da 'yan kasar Iraki suke fuskanta.
Alkaluma na baya baya sun shafi adadin mutanen da rikicin ya rutsa da su cikin rahoton tawagar ba da tallafi ta MDD dake Iraki (UNAMI).
Tawagar UNAMI ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, mutane 559 da suka mutu a cikin watan Oktoba, dukkansu fararen hula ne, da 'yan sanda da ba su sa kayan 'yan sanda ba, a yayin da kuma 155 suka kasance jami'an tsaron kasar Iraki, da dakarun musammun na SWAT na ma'aikatar cikin gida da mayakan sa kai dake taimakawa rundunar sojojin Iraki wajen yaki. (Maman Ada)