in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da zazzabin Lassa ya hallaka a Najeriya ya karu zuwa 63
2016-01-21 11:27:41 cri

Kafofin watsa labaru a Najeriya sun ba da rahoto a jiya Laraba cewa, mutane 212 ne suka kamu da zazzabin Lassa tun bayan barkewar cutar a watan Nuwamba na shekarar bara, kuma daga cikin adadin mutune 63 sun hallaka.

Ministan kiwon lafiya na kasar Isaac Adewole, ya fada a taron gaggawa kan harkokin kiwon lafiya da aka yi a ranar 19 ga wannan wata a Abuja hedkwatar kasar cewa, zazzabin Lassa ya samu yaduwa zuwa jihohi 17 na kasar.

Isaac Adewole ya zargi wasu jihohin kasar da boye hakikanin adadin mutanen da zazzabin ya kashe. Sannan ya gargadi jami'an kiwon lafiya na wurare dabam dabam a kasar, da su kara sa ido domin dakile yaduwar zazzabin, da kuma daukar matakan rigakafi, don samun nasarar kau da cutar zazzabin cikin wannan shekara.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China