in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gurfanar da jami'ai 55 gaban kuliya a Najeriya
2016-01-19 09:42:55 cri

Ministan watsa labarai a Najeriya Lai Mohammed, ya ce, nan da 'yan kwanaki za a gurfanar da wasu manyan jami'an tsohuwar gwamnatin kasar da ta gabata su 55 gaban kuliya, bisa zargin aikata badakalar kudaden hukuma.

Lai Mohammed wanda ya bayyana hakan yayin wani taron 'yan jaridu a jiya Litinin, ya ce, alkaluma sun nuna yadda aka wawashe kudade har kimanin dalar Amurka biliyan 6.72, sama da kashi daya bisa hudu na daukacin kasafin kudin shekarar bara. Ministan ya ce, an aikata wannan ta'asa ne tsakanin shekarun 2006 zuwa 2013.

Kaza lika a cewar Mr. Mohammed, cikin manyan jami'an da za su gurfana gaban kuliya, akwai tsaffin gwamnoni 15, da ministoci 4, tare da ma'aikatan gwamnatin tarayya da na jahohi 12.

Baya ga wadannan jami'ai 55 da za su bayyana gaban kuliya daga tsohuwar gwamnatin, akwai kuma wasu 'yan Najeriyar da yanzu haka ake bincikar su bisa zargin rub da ciki kan kudaden sayen makamai, kudaden da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 2, wadanda kuma ake zargin an karkatar da su zuwa lalitar wasu daidaikun 'yan kasar.

Mr. Mohammed ya kara da cewa, tuni aka fara dawo da wasu daga wadannan kudade zuwa lalitar gwamnati.

Sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa, matakin da gwamnatin ta ce ta dauke shi ne domin hana kasar karasa durkushewa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China