in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin kan Sin da Najeriya a fannin kimiyya zai ba da damar cin moriya
2016-01-14 10:50:56 cri

Ministan ma'aikatar kimiyya da fasaha na Najeriya Ogbonnaya Onu ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a Larabar nan cewar, a yayin da huldar dake tsakanin kasar Sin da Najeriya ta kai wani babban matsayi ta fuskar bunkasuwa a fannin kimiyya da fasaha, hakan zai baiwa bangarorin biyu samun moriya.

Tawagar manyan jami'an gwamnatin Najeriyar zai halarci taron tattaunawa da takwarorin su na kasar Sin da kuma hadaddiyar tawagar hukumomi masu zaman kansu.

Minnistan ya ce, ya yi amanna cewar, Najeriya za ta koyi darrusa masu yawa a sakamakon huldar dangantaka da babbar kasa kamar Sin. Mista Onu ya fada a Abuja gabannin ziyarar sa zuwa Sin cewar, taron tattaunawar da za'a gudanar da takwarorin sa na kasar Sin zai kara dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu, musamman a bangaren kimiyya da fasaha.

Ya kara da cewar, wannan ziyara za ta kasance tamkar wata dama ce da za ta kara janyo hankalin masu zuba jari daga kasar Sin zuwa Najeriyar, wacce ke sahun gaba ta fuskar karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika. Kuma akwai bukatar yin amfani da kimiyya da fasahar wajen inganta rayuwar al'umma.

Ministan ya ce, Najeriya a shirya take ta kulla yarjejeniya da kasar Sin wajen musayar fasaha da samar da kwarewa ga ma'aikata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China