Yan tawayen ADF na kasar Uganda sun kaddamar da wani hari da manyan makamai tun cikin daren ranar Asabar kan wani sansanin sojan rundunar Congo na Linzo Sisene, wani kauyen na yankin Beni dake fiye da a kalla kilomita 50 daga arewa maso gabashin birnin Beni, a gabashin DRC-Congo.
Har yanzu babu wani adadin da ya fito na mutuwa ko jikkata daga filin dagar. Sai dai a cewar wasu majiyoyin soja, sojojin rundunar FARDC sun ci nasarar dakile harin maharan na ADF.
Majiyoyin soja na FARDC sun tabbatar da cewa, maharan sun yi yunkurin karbe ikon sansanin sojan rundunar dake wurin domin neman makamai da harsasai.
Tun ranar Lahadi da safe, rundunar sojoji ta FARDC ta ci gaba da farautar maharan, a cewar majiyoyin dake wurin. (Maman Ada)