Rundunar sojojin kasar Uganda ta fada jiya Alhamis cewar, ba gaskiya ba ne rahotonni dake cewar mayakan Al-Shabsab sun yi garkuwa da sojojinta a Somaliya wadanda ke aiki a rundunar hadin gwiwa don wanzar da zaman lafiya ta kungiyar hada kan Afrika wato AMISOM.
A ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar Al-Shabaab ta kai hari a wani sansanin sojan tawagar AMISOM a Somaliya, yayin da a ranar Laraba mai magana da yawun kungiyar Abdiaziz Abu Muga ya yi ikirarin cewar, mayakan na tsare da dakarun Uganda.
Sai dai kakakin rundunar sojan na Uganda Col. Paddy Ankunda ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ta waya cewar, ikirarin da kungiyar Al-shabaab ta yi na yin garkuwa da sojojin Uganda karya ce, kuma tawagar AMISON ta riga ta yi bayani kan wannan.
Sai dai ya bayyana cewar, kimanin sojojin Ugandan 12 suka gamu da ajalinsu a yayin harin.(Ahmad Fagam)