Kasar Uganda ta bayyana cewa, kasashe ba neman gaggauta cimma daukar matakan soja za su yi ba domin warware matsalar kaifin kishin addini a Afrika, abin muhimmaci shi ne su auna dalilan dake janyo hakan yadda ya kamata.
Kasar Uganda ta zo karshen wa'adinta na shekara guda a matsayin shugabar babban taron MDD karo na 69 (AGNU), kana shekaru biyu da suka gabata da kasar ta shugabanci kwamitin tsaro na MDD a matsayin mamba ba ta din din din ba. Haka kuma, kasar ta kasance mamba ta kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika (AU). (Maman Ada)