Alkaluman hukumar kwastam na nuna cewa, kasar Sin ta kasance ta farko cikin watanni 11 na farkon shekara ta 2014 wajen samar da kayayyaki a kasar Aljeriya.
Rahotanni na cewa, darajar kayayyakin da Sin ta samar a kasar ta Aljeriya ta kai dala biliyan 7.44, sai kasar Faransa da ke biye mata baya da kayayyakin da suka kai darajar dala biliyan 5.89.
Bugu da kari a karon farko a shekara ta 2013, kasar ta Sin ta dara kasar Faransa a bunkasa bangaren kayayyakin da ba su shafi mai ba da darajarsu ta kai sama da dala biliyan 8.
A watan Fabrairun shekarar 2014 ne kasashen Sin da Aljeriya suka daga matsayin hadin gwiwar da ke tsakaninsu, wadda ta kasance irinta ta farko tsakanin dangantakar da Sin ta kulla da kasashen Larabawa. (Ibrahim)