in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibia na samun karin Sinawa 'yan yawon shakatawa
2015-06-23 10:41:32 cri

Hukuma mai kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Namibia ko NTB a takaice, ta ce, yanzu haka yawan Sinawa masu zuwa kasar domin yawon bude ido na karuwa sannu a hankali.

Wasu alkaluma da NTBn ta fitar, sun nuna cewa, a shekarar bara yawon Sinawa da suka ziyarci kasar ya kai mutane 11,583, sabanin Sinawa 9,910 da kasar ta karba a shakarar 2013.

Yawon shakatawa dai ita ce babbar harka dake samarwa Namibia kudaden shiga, inda a duk shekara ta kan samu kudaden shiga kimanin dalar Amurka miliyan 590, daga 'yan yawon bude ido dake zuwa kasar, su kimanin miliyan daya da dubu dari uku.

Kasashen da al'ummarsu suka fi zuwa Namibia sun hada da Afirka ta Kudu, da Jamus, da Birtaniya, da Italiya, da Faransa da kuma al'ummar kasar Sin wadanda a yanzu haka yawansu ke dada karuwa.

A cikin watan Disambar bara, cibiyar "Lonely Planet" ta bayyana kasar Namibia a matsayin kasa ta 5 mafi kayatarwa a fannin yawon bude ido a duk duniya.

Yanzu haka dai hukumar NTB na mai da hankali ga tallata Namibia a biranen kasar Sin dake da rinjayen masu matsakaicin samu, kamar biranen Shanghai, da Beijing, da Guangzhou, da Shenzhen, da Tianjin da Chongqing, domin kara janyo hankalin Sinawa zuwa kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China