in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron dandalin tattaunawa na hadin gwiwar kafofin watsa labaru a tsakanin Sin da kasashen Larabawa a birnin Cairo
2016-01-19 09:35:26 cri
An kammala taron dandalin tattaunawa na hadin gwiwar kafofin watsa labaru a tsakanin Sin da kasashen Larabawa a birnin Cairo a jiya Litinin. Kimanin shugabannin kafofin watsa labaru 42 na kasar Sin da na kasashen Larabawa ne suka halarci taron, inda suka tattauna kan inganta hadin gwiwarsu a fannin aikin jarida.

Darektan ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Jiang Jianguo, ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana cewa a shekarun baya, an kafa dandalin tattauanawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Larabawa, tare da samun kyakkyawan sakamako, bangarorin biyu sun kuma hada kan juna kan wasu muhimman batutuwa na kasa da kasa da na shiyya-shiyya, har ma sun zama abin koyi a fannin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Mr. Jiang yana fatan kafofin watsa labaru na bangarorin biyu za su maida hankali wajen yada labaran da suka bayyana burin al'umma na samun zaman lafiya da bunkasuwa, tare da sa kaimin yin musayar al'adu da kuma karfafa dankon zumunci a tsakanin sassan biyu.

Babban editan jaridar Al Ahram Mohamed Ibrahim Desoky ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, kafofin watsa labaru suna taka muhimmiyar rawa a fannin raya hulda a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, za a kuma ci gaba da inganta shi ta hanyoyi biyar, wato na farko, kara tura manema labaru yin aiki da juna da kara yawan kafofin watsa labaru na kasashen Larabawa dake kasar Sin. Na biyu, kara yin musayar ra'ayi kan harkokin gudanar da kafofin watsa labarai. Na uku, tabbatar da kafofin watsa labaru wajen bada muhimmanci kan tarihi da al'adun gargajiya na jama'ar bangarorin biyu domin kara fahimtar juna. Na hudu, kara yin musayar ra'ayi a fannonin kimiyya da fasaha da kuma al'adu. Na biyar, kara yin hadin gwiwa a tsakanin manyan kamfanonin jaridu a tsakaninsu. Na shida, kara yin musayar ra'ayi kan sinima da wasannin kwaikwayo.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China