in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya za ta kaddamar da gaggarumin aikin ci gaba
2016-01-13 09:28:51 cri

Gwamnatin Nigeriya ta ce, ba da dadewa ba za ta kaddamar da gaggaruman ayyukan inganta ci gaba a kasar, kamar yadda mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar a ranar Talatan nan a garin Kaduna dake arewacin kasar, lokacin kaddamar da ginin sabbin gidajen kwana 2,000 da babban shago wanda gwamnatin jihar ta kirkiro.

Ya ce, gwamnatin tarayya za ta zuba karfin ta wajen samar da gidajen zama da sauran kayayyakin more rayuwa don inganta rayuwan al'umman kasar.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, gwamnati tana da kuduri mai kyau na aiwatar da mulki da kyau da zai samar da kayayyakin more rayuwa ga al'ummar sa. Ya ce, inda aka dubi irin nau'in gidajen jama'a a fadin kasar, gwamnatocin jihohi kadan ne suka iya kaddamar da gidaje guda 1,000 a lokaci daya.

Tun da farko gwamnan jihar malam Nasiru El-Rufai ya ce, za'a aiwatar da aikin ginin ne ta hadin gwiwwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu saboda gwamnatin jihar ita kadai ba za ta iya aiwatar da aikin ba da kudin ta.

Ya yi bayanin cewa, gidajen guda 2,000 da suka hada da masu dakuna biyu da masu dakuna uku za'a kammala su ne a cikin watanni 12, kuma bayan an kammala, za'a ba da gidajen ga ma'aikatan gwamnati da sauran jama'a wadanda za su biya na dukunan biyu da uku a cikin shekaru 15 zuwa 20 .

A game da babban shagon kuma, gwamna El-Rufai ya ce, za'a yi shi ne domin inganta ciniki da ayyukan tattalin arziki a jihar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China