in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafa bankin AIIB zai sa kaimi ga raya muhimman ababen more rayuwa a Indonesiya
2016-01-11 11:36:31 cri

Shugaban Asusun kudu maso gabashin nahiyar Asiya na kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN a reshen kasar Indonesiya Li Zhuohui ya bayyana a ranar 10 ga wata cewa, bankin saka jari kan muhimman ababen more rayuwa na kasashen Asiya wato AIIB da za a bude a ranar 16 ga wata a hukunce a birnin Beijing zai sa kaimi ga raya muhimman ababen more rayuwa a kasar ta Indonesiya.

Li Zhuohui ya ce, kafa bankin AIIB ya samu goyon bayan kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya har ma da wasu kasashe sama da 50 daga nahiyoyi 5 na duniya, kuma zai zama wani sabon tsarin hada-hadar kudi na kasashen duniya, wadanda suke taka rawa wajen kafa sabon tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa, matakin da ke nuna cewa, tunanin yin gyare-gyare da kirkiro da sabbin abubuwa da shugabannin kasar Sin suka gabatar yana taka muhimmiyar rawa a duniya, kuma yana canja tsohon tsarin tattalin arziki da kasashen yammacin duniya suka yiwa babakere. Ya yi imani da cewa, bankin AIIB da sauran sabbin hukumomin hada-hadar kudi suna kara habaka, hakan da zai taimakawa kasashe masu tasowa, ciki had da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, kuma zai inganta hadin gwiwar kasashen da ke yanki, da raya muhimman ababen more rayuwa a wadannan kasashe.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China