Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin kasar Sin, musamman wajen inganta fannin sufurin jiragen kasa.
Ministan sufurin kasar Rotimi Amaechi, shi ne ya tabbatar da hakan a yayin da jakadan kasar Sin a Najeriya Gu Xiaojie, ya ziyarce shi a ofishinsa dake Abuja, babban birnin kasar.
Ministan ya yaba wa kasar Sin dangane da irin tallafin da take baiwa gwamnatin Najeriya a fannin samar da ababan more rayuwa, musamman bangaren sufurin jiragen kasa.
Amaechi, ya kara da cewar, duk da kasancewar an gudanar da ayyuka masu yawa, amma har yanzu Najeriya na bukatar a kammala wasu ayyuka da aka fara su.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers a shiyyar kudu maso gabashin kasar, ya bukaci hada gwiwa da gwamnatin kasar Sin don hanzarta kammala aikin ginin hanyar jirgin kasa.
Jakada Gu, ya ce, kasar Sin ta cimma nasarori masu yawa wajen samar da ababan more rayuwa a Najeriyar, kuma za ta ninka kokarinta, sannan ya bayyana cewar, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da hada gwiwa da Najeriya wajen bunkasa masana'antun kasar.(Ahmed Fagam)