Kamfanin gine-gine na kasar Sin CCECC, ya kammala wani katafaren aiki na fadada titin mota, da samar da hanyar motocin bas, a jihar Legas dake kudancin Najeriya.
Mahukuntan jihar dai sun bayyana cewa, aikin zai saukakawa miliyoyin al'ummar jihar wahalhalun da suke fuskanta ta fuskar sufurin ababen hawa.
Da yake jawabi yayin bikin bude babbar hanyar wanda aka gudanar jiya Alhamis a tashar Majidun dake unguwar Ikorudu, gwamnan jihar ta Legas Akinwunmi Ambode, ya ce, aikin ya nuna irin aniyar da gwamnati ke da ita ta samar da ababen more rayuwa ga al'umma. Ya kuma godewa kamfanin CCECC bisa managarcin aikin da ya gudanar.
Shi ma a nasa jawabin, jagoran kamfanin na CCECC a Najeriya Li Qingyong, cewa ya yi kammala aikin zai baiwa masu ababen hawa damar rage tsawon lokaci da suke bukata a lokutan zirga-zirga.
Manyan baki da suka halarci bikin kaddamar da sabuwar hanyar sun hada da kusa a jam'iyya mai mulki a Najeriya, kuma tsohon gwamnan jihar Bola Ahmad Tinubu, da gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola da dai sauran su.(Saminu)