in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Najeriya za su kara bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu
2015-12-03 09:49:15 cri

Gwamnatin Najeriya ta bayyana kudurin ta na kara bunkasa dangantakar da ke tsakanin ta da kasar Sin yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ke tafe a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Shugaba Muhammed Buhari na Najeriya ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda ya bayyana shirinsa na sake bibiyar abubuwan da suka tattauna da takwaransa na kasar Sin a lokacin babban taron MDD da ya gudana a watan Satumban da ya gabata.

A yayin wancan ganawa, shugaba Buhari ya shaidawa takwaransa na kasar Sin Xi Jinping bukatar sake maido da aikin shimfida layin dogo, inda a wannan karon kasar Sin za ta tallafa da kudin gudanar da aikin.

Ko da yake sanarwar musamman tana son ganin an gudanar da aikin shimfida layin dogo da zai hade Legas da Kalaba mai tsawon kilomita 1,402, aikin da ake sa ran zai lashe tsabar kudi dala biliyan 12, baya ga guraben aiki kimanin 200,000 da ake fatan zai samar.

A ranar Alhamis ne ake sa ran shugaban na Najeriya zai tashi zuwa kasar Afirka ta Kudu don halartar taron na FOCAC. Daga cikin wadanda za su rufa masa sun hada da ministocin harkokin kasashen waje da na cikin gida, harkokin sufuri, masana'antu, cinikayya da zuba jari.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China