in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DA ta bukaci SAFA da ta yi karin haske game da zargin da ake mata na baiwa FIFA cin hanci
2015-06-02 09:53:45 cri

A jiya ne jam'iyyar adawa ta DA da ke kasar Afirka ta Kudu ta bukaci hukumar kwallon kafar kasar SAFA da ta yi karin haske game da zargin da ake mata na baiwa hukumar kwallon kafar duniya FIFA cin hanci don samun nasarar karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta shekarar 2010.

Wannan batu na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaban hukumar kwallon kafar kasar (SAFA) Danny Jordaan ke tabbatar da cewa, hakika an baiwa hukumar kwallon kafa ta arewaci, tsakiyar Amurka da Karebiyan (CONCACAF) kudin da ya kai dala miliyan 10, amma ya ce, kudaden ba cin hanci ba ne, illa wani kokari na taimakawa ci gaban harkokinsu na kwallon kafa.

A jawabinsa, ministan wasanni da walwalar jama'a na kasar Afirka ta Kudu Solomon Malatsi ya ce, zargin da ake yiwa kasar na karbar cin hanci bai dakusar da gasar da aka gudanar a kasar ba, amma 'yan Afirka ta Kudu na bukatar sanin dalilin da ya sa kwamitin shirya karbar gasar (LOC) ya baiwa hukumar CONCACAF wadannan kudade a shekarar 2008 bisa amincewar wakilin kasar kuma da sunan kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China